# Gwamna ya yi magana kan rikicin iyali da shari'a a Abuja

- Original post: https://www.twitter.com/i/status/2124382595647418723
- Source account: [@bbchausa](https://x.com/bbchausa)
- Source language: Filipino
- Target language: Hausa
- Duration: 1:32
- Published: 2026-11-22
- Machine translated. Check the original before quoting.
- Canonical URL: https://www.translate.mom/transcript/ftIXLkc6Ow9n/ha/gwamna-ya-yi-magana-kan-rikicin-iyali-da-shari-a-a-abuja
- Original-language version: https://www.translate.mom/transcript/ftIXLkc6Ow9n/tl/gobernador-nagsalita-sa-alitan-ng-pamilya-at-kaso-sa-abuja.md

## Transcript

[0:00](https://www.translate.mom/transcript/ftIXLkc6Ow9n/ha/gwamna-ya-yi-magana-kan-rikicin-iyali-da-shari-a-a-abuja) A irin wannan batun iyali, abu ne mai matuƙar wahala, wanda Bature ke cewa very sensitive, uh, issue.

[0:11](https://www.translate.mom/transcript/ftIXLkc6Ow9n/ha/gwamna-ya-yi-magana-kan-rikicin-iyali-da-shari-a-a-abuja?t=11) To, matsalar ita ce idan siyasa ta shiga, bai kamata siyasa ta riƙa shiga ba.

[0:19](https://www.translate.mom/transcript/ftIXLkc6Ow9n/ha/gwamna-ya-yi-magana-kan-rikicin-iyali-da-shari-a-a-abuja?t=19) Sai abubuwa suka faru, ana ganinta a matsayin, wato, 'yarsa ce, ni kuma a matsayina na miji, sai ka ga ya sa ta kai ni ƙara a kotu.

[0:34](https://www.translate.mom/transcript/ftIXLkc6Ow9n/ha/gwamna-ya-yi-magana-kan-rikicin-iyali-da-shari-a-a-abuja?t=34) Kuma kotun ba a Kano take ba, kotun tana Abuja.

[0:37](https://www.translate.mom/transcript/ftIXLkc6Ow9n/ha/gwamna-ya-yi-magana-kan-rikicin-iyali-da-shari-a-a-abuja?t=37) Kuma abu ne da ba mu sani ba, ya zama mana kamar sabon abu.

[0:43](https://www.translate.mom/transcript/ftIXLkc6Ow9n/ha/gwamna-ya-yi-magana-kan-rikicin-iyali-da-shari-a-a-abuja?t=43) To, ni a matsayina na gwamna, ga yarana, ga ni, da irin waɗannan abubuwa.

[0:48](https://www.translate.mom/transcript/ftIXLkc6Ow9n/ha/gwamna-ya-yi-magana-kan-rikicin-iyali-da-shari-a-a-abuja?t=48) Amma a matsayinka na babba, ana ganin bai kamata ka mayar da batun iyalinka siyasa ba a gaban mutane.

[0:54](https://www.translate.mom/transcript/ftIXLkc6Ow9n/ha/gwamna-ya-yi-magana-kan-rikicin-iyali-da-shari-a-a-abuja?t=54) Ai ba ni na mayar da shi siyasa ba. Abin da ke faruwa shi ne, yadda abin ya faru.

[1:02](https://www.translate.mom/transcript/ftIXLkc6Ow9n/ha/gwamna-ya-yi-magana-kan-rikicin-iyali-da-shari-a-a-abuja?t=62) Kai, yanzu idan aka maka haka, za ka ji daɗi?

[1:05](https://www.translate.mom/transcript/ftIXLkc6Ow9n/ha/gwamna-ya-yi-magana-kan-rikicin-iyali-da-shari-a-a-abuja?t=65) A kwashe iyalinka ba tare da saninka ba, Saboda an ɗauke ta ne aka kuma aka yi abin da ake kira garkuwa da mutum.

[1:15](https://www.translate.mom/transcript/ftIXLkc6Ow9n/ha/gwamna-ya-yi-magana-kan-rikicin-iyali-da-shari-a-a-abuja?t=75) Kamar dai yanzu kuka fara magana tsakaninku, ina ganin akwai matsala.

[1:18](https://www.translate.mom/transcript/ftIXLkc6Ow9n/ha/gwamna-ya-yi-magana-kan-rikicin-iyali-da-shari-a-a-abuja?t=78) To, ka ga tun da tana kotu, to muna taka-tsantsan, muna jira mu ji.

[1:25](https://www.translate.mom/transcript/ftIXLkc6Ow9n/ha/gwamna-ya-yi-magana-kan-rikicin-iyali-da-shari-a-a-abuja?t=85) Eh, amma Mai Girma, da gaske kun rabu da ita?

[1:28](https://www.translate.mom/transcript/ftIXLkc6Ow9n/ha/gwamna-ya-yi-magana-kan-rikicin-iyali-da-shari-a-a-abuja?t=88) Me kake nufi? A matsayinta na matarka, da gaske kun rabu?
